Change in life is constant. Change always comes with negative or positive effect. Whenever there is change, there is need to adjust in order to stabilize situations in the society.
What happens, when the effort to make adjustment seems abortive?
How do you feel when the conditions are unfavourable and you are incapacitated to make adjustments?
#Dama Is an expression of feelings
#Dama reveals the only and reliable solution to the unfavourable circumstances in a society
-DAMA-
Verse1:Wani lokaci kamar dai in koma ciki,
Ciki na uwata can babu bakinciki.
Da zan samu dama da zanje inyi kwanaki,
Can babu mugunta kuma babu munafuki.
Bridge: Ina ma, ina ma, da can hamada nake,
Don cikin jama'ata zubarda jini ake.
Dazan Sami dama da a ruwa nake,
Mazanmu da mata munafunci ake.
Chorus:Da zan Sami dama, wa zai ba-ni dama,
Da zan sami dama, dazan dai- na fama.
Verse2: Zaman duniya,zamani zabi take
Wasu da arziki ga wasu can wahala suke.
Abinda zasuci, dakyar suke ku-ka suke,
Wasu ko zasuci,dakyar su kal-li inda suke.
(Bridge, chorus and interlude)
Verse3:Ga wasu basu zama a gida jeji suka kwana,
An kona gidanjensu gasu a yunwace.
Ga wata babu miji yaya kuma sun rasa baba,
Don rashin tsaro a kasa yanzu ga wasu sun mace.
Ya ubangiji...yanzu mun gaji...
Kayi agaji...karabamu da masu mugunta.
( chorus with this👇)
Da zan Sami dama da zan koma ciki,
Inyita sharar barci babu ruwana da knowa.
Inama, inama da hamada nake,
Da zan zauna shiruuuu babu ruwana da kowa.
Da zan Sami dama da a ruwa nake,
Inyita bandam- bandam babu ruwana da kowa.